30 Yuni 2021 - 13:09
​Iran:Ma’aikatar Kiwon Lafiya Ta Bawa Alluran Riga Kafin Cutar Covid19 Na Biyu Lasisin Fara Amfani Da Ita

Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Iran ta bada lasisi ga alluran riga kafin cutar Covid 19 wacce hadin guiwan masana na cikin gida da na kasar Cuba suka samar da ita.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Iran Press (IP) ya nakalto ministan kiwon lafiya na kasar Saeed Namaki ya na bada wannan sanarwan a jiya Talata.

Wannan dai ita ce alluran riga kafin cutar korona na biyu wacce ta sami lasisin amfani da ita a cikin kasar Iran.

Ministan ya kara da cewa an kammala dukkan ayyukan gwaje-gwajen alluran riga kafin a dukkanin marhalolin gwajinta, daga ciki har da gwaji kan mutane 44,000 a kasar Cuba da kuma wasu 25,000 a kasar Iran.

Ministan ya kammala da cewa kwararo a hukumar abinci da magunguna sun tabbatar da ingancin alluran, wanda ya sa aka sanya ta cikin jerin alluran riga kafin cutar korona wadanda za’a yi amfani da su a cikin gida.

342/